Wutar lantarki ta fi arha a Nijeriya fiye da kasar Senegal, in ji kamfanin TCN

-

Kamfanin rarraba wutar lantarki a Nijeriya TCN ya ce duk da karin kudin lantarki da aka samu, amma kasar ta fi wasu kasashe makwabtanta sauki da arha wajen biyan kudin wutar lantarki.
Manajan Daraktan kamfanin Sule Abdul’aziz ya sanar da hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
Ya ce farashin da ‘yan Nijeriya ke biya na kudin wutar lantarki ba tsada bace, kawai dai yanayin samar da wutar ne ke da aiki babba, musamman batun canjin Dala da sauran kudaden kasashen waje.
Ya ce idan aka kwatanta da kasashe irinsu Nijar, Mali, Togo da Senegal, za a ga cewa ‘yan Nijeriya kukan-dadi suke yi kan batun farashin wutar lantarki.
Sule Abdul’aziz ya ba da tabbacin cewa ‘yan Nijeriya za su iya samun tsayayyiya kuma wadatacciyar wutar lantarki nan da shekaru 5 masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara