DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun yi ajalin ‘yan sanda hudu a Katsina

-

Wasu bayanai da DCL Hausa ta tattara sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari ga jami’an ‘yan sanda da ke aikin samar da tsaro a yankin ‘Yar Tsamiyar Jino cikin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida cewa lamarin da ya faru da misalin karfe 3:43 na yammacin Talatar nan, ya yi sanadiyyar ajalin jami’an ‘yan sanda hudu, sun kuma kona motar daya da jami’an tsaron ke aiki da ita.
Majiyar ta ce ‘yan sandan na kwantar da tarzoma wato ‘mopol’ sun hadu da ajalinsu ne a lokacin da barayin dajin suka yi wa inda suke aiki kawanya a cikin wata makarantar firamare ta kauyen na ‘Yar Tsamiyar Jino.
Haka kuma, barayin dajin sun hallaka mutane biyu fararen hula ‘yan garin ‘Yar Tsamiyar Jino.
Kazalika, bayanai sun ce maharan sun kwashi makamai da ake kyautata zaton mallakin jami’an tsaron ne, sun kuma cinna wa aji daya wuta a cikin makarantar.
Wani mazaunin kauyen Mai Dabino da ke makwabtaka da ‘Yar Tsamiyar Jino da ya zanta da DCL Hausa da shi ma ya bukaci a sakaya sunansa ya ce da farko ‘yan bindigar sun yi niyyar kai wa masu zuwa kasuwar Kankara daga Mai Dabino hari ne, da mutanen suka ji labari sai suka ki zuwa kasuwar. Ya ce da barayin suka ji ‘yan Mai Dabino sun fasa zuwa kasuwar ne sai suka sauya alakar harinsu zuwa ga kauyen na ‘Yar Tsamiyar Jino.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta hannun kakakinta ASP Sadiq Aliyu Abubakar ta tabbatar wa da DCL Hausa faruwar lamarin, inda ta ce jami’an ta hudu sun riga mu gidan gaskiya ta dalilin harin na ‘yan ta’adda a kauyen na ‘Yar Tsamiyar Jino.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin kasar na kan hanyar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 cikin shekaru goma masu zuwa. Kashim...

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da direba da fasinjoji a Katsina

Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau a Katsina. Jami’an sun yi artabu da ‘yan...

Mafi Shahara