![]() |
Hoton Kamfanin |
Kamfanin Orano mallakin kasar Faransa mai hakar uranium a Nijar ya sanar da ranar 31 ga watan Oktoban nan a matsayin ranar da zai dakatar da ayyukan sa
Wata mai magana da yawun kamfanin ce daga birnin Paris ta sanar da hakan, inda ta ce matsalolin da kamfanin ke fuskanta ne za su tilasta masa dakatar da aikin
Cikin matsalolin da ta zayyana mai magana da yawun kamfanin ta ce har da na rashin hanyar fitar da shi zuwa ga abokan cinikayya kuma sun shawararci hukumomin Nijar din da su yi amfani ta hanyar sama ta Namibie amma ba su samu amsa ba.
Kamfanin ya ce a yanzu haka yana da akalla tan 1,050 na uranium din a jibge ba tare da an samu damar fitar da shi ba wanda ya kai darajar kudi yuro milyan 300.