HomeUncategorizedKu gaggauta kamo Bello Turji a mace ko a raye - Ministan...

Ku gaggauta kamo Bello Turji a mace ko a raye – Ministan tsaro ya bukaci sojoji

-

 

Muhammad Badaru/Bello Matawalle

Ministan tsaron Nijeriya Mohammed Badaru ya umarci dakarun Operation Fansar Yamma da su kamo dan ta’addar nan Bello Turji da ake nema ruwa a jallo.

Minisna ya ba da wannan umarnin ne sa’o’i 24 bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wasu sauye-sauye ga ministocinsa.  

Da yake jawabi ga sojojin a barikin One Brigade Headquarters da ke Gusau a jihar Zamfara a ranar Alhamis, Badaru ya kara wa sojojin kwarin gwiwa, inda ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya bibiyi ayyukansu a cikin ‘yan watannin da suka gabata kuma ya fahimci an samu ci-gaba.

Ministan ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya bukaci ya gode wa jami’an sojin tare da kara rokar su da su kara himma wajen kawo karshen rashin tsaro a wadannan yankunan da ake gudanar da ayyukan ta’addanci da kuma kasa baki daya.

A cewarsa, Shugaba Tinubu a shirye yake ya samar da duk abin da suke bukata don kawo karshen rashin tsaro a Arewa maso Yamma da Najeriya baki daya.

Badaru Abubakar ya ce ya samu tabbaci daga kwamandan da ke kula da shiyyar kuma ya bayyana farin-cikinsa da tabbacin cewa za su samu nasara, ya kuma bukaci jami’an sojin da su kamo Bello Turji.

Kalaman Badaru na zuwa ne makonni uku bayan da babban hafsan hafsan tsaron kasa(CDS) Janar Christopher Musa, ya ce kwanakin Turji sun kusa karewa.

A cewar CDS, sabbin hare-haren da sojoji suka sake kaiwa kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma sun jefa fargaba a ga dan ta’adda Turji da mutanensa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img