HomeUncategorizedMa'aikatan lafiya sun tafi yajin aikin gargadi na kwanaki 7

Ma’aikatan lafiya sun tafi yajin aikin gargadi na kwanaki 7

-

Likitoci

Kungiyoyin hadin gwiwa na bangaren lafiya JOHESU da kwararrun ma’aikatan lafiya sun sanar da fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, wanda zai fara da tsakar daren Juma’a 25 ga Oktoba, 2024.

Matakin ya biyo bayan cikar wa’adin kwanaki 15 da aka baiwa gwamnatin tarayya a baya kan bukatun da ma’aikatan lafiyar ke nema.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, shugaban kungiyar JOHESU na kasa, Kabiru Minjibir, ya bayyana muhimman bukatun kungiyar, wadanda suka hada da aiwatar da tsarin tsarin albashi mai tsoka ga ma’aikatan lafiya,da kuma sake fasalin shekarun ritaya ga ma’aikatan kiwon lafiya,sauran buÆ™atun sun haÉ—a da biyan alawus-alawus É—in ma’aikatan kiwon lafiya.   

Yajin aikin na gargadin dai na iya kawo cikas ga ayyukan kiwon lafiya a fadin kasar, musamman a manyan cibiyoyin kiwon lafiyar al’umma.

Yajin aikin na baya-bayan nan da kungiyar ta JOHESU ta yi ya biyo bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya ta yi, wanda da yawa daga cikinsu ba a samu sakamako mai kyau ba.Kungiyar dai ta ba da shawarar inganta yanayin aiki ga kwararrun masana kiwon lafiya, musamman dangane da gudummawar da suka bayar yayin afkuwar cutar COVID-19.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img