Binciken jaridar Daily Trust ta gano cewa yawan cin namijin-goron da ake yi a halin yanzu da kuma yawan fitar da shi zuwa kasashen waje ne ya sa ya yi tsada.
Rahoton jaridar dai ya ce a baya mutane ba su damu da shi ba, saboda ba kowa ne ke amfani da shi ba, amma a halin da ake ciki namijin-goron ya fara wuya saboda yawan fitar da shi zuwa kasashe irinsu China, Indonesia, Thailand, Japan da karin kasashen nahiyar Asia.
Wani falken goro a kasuwar ‘yan goro ta Mariri a Kano Alhaji Usman Dauda ya ce yanzu har a kasashen duniya ma neman namijin-goron ake yi sosai.
Binciken ya gano cewa mafi yawa ‘yan Arewa ne ke cin namijin-goron duk kuwa da a yankin ba a nomansa, an fi nomansa a yankin Kudu maso Kudu, Kudu maso Arewa da wani yanki na Arewa ta tsakiyar Nijeriya.