Kungiyoyin ma’aikatan jami’a da ba malamai ba NASU, SSANU za su tsunduma yajin aiki sai baba ta gani daga ranar Litinin
Hakan na zuwa ne bayan dogon wa’adin da kungiyoyin suka ba gwamnatin kasar domin ta biya su albashin watanni hudu da suke bi bashi
Ma’aikatan sun yi yajin aiki a 2022 lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari inda aka sanya musu dokar babu aiki ba biya har tsawon watanni hudu