DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Dole ne gwamnati ta biya diyyar asarorin da aka yi ta dalilin lalacewar wutar lantarkin Arewacin Nijeriya – PRP

-

Jami’iyyar PRP a jihar Katsina ta yi barazanar garzayawa kotu don kalubalantar gwamnatin tarayya bayan da wutar lantarkin Arewacin Nijeriya ta lalace.
Jami’iyyar ta yi zargin cewa sakacin gwamnatin tarayya ne ya sa aka samu wannan matsalar da yanzu haka ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da jaza asarori ga kasuwancin da ake gudanarwa a yankin.
Jami’iyyar ta yi wannan barazanar ne ta hannun dan takararta na Gwamnan jihar Katsina a zaben 2023 Imran Jino a lokacin da ya gudanar da taron manema labarai a Katsina.
Sai dai, Imran Jino ya ce jami’iyyar za ta fitar da ‘form’ da za a yi amfani da shi don gano hakikanin mutanen da suka rasu ta dalilin wannan matsalar wutar lantarki kafin su garzaya kotu neman hakkin wadannan mutane daga gwamnatin tarayya.
Ya yi takaicin cewa KO asibitoci da dakunan gwaje-gwaje da a kodayaushe suke bukatar lantarki dawwamamme, sun shiga halin ni-‘ya-su ta dalilai n katsewar wutar.
Imran Jino ya ce wannan matsala ta durkusar da kananan kasuwanci tare da tagayyara iyalai da dama a jihar Katsina da ma sauran sassan Arewacin Nijeriya da lamari ya rutsa da shi.
Jami’iyyar ta PRP ta ce ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta biya diyya GA waÉ—anda suka samu asarori ta dalilin lalacewar wutar lantarkin Arewacin Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara