DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a yi amfani da jiragen soji wajen bai wa masu gyaran lantarkin Arewa kariya-Abdulaziz Abdulaziz

-

 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu

Tun bayan da Shugaban Tinubu ya nuna fushinsa kan yadda rashin wuta ya addabi yankin Arewa har ya bayar da Umarnin Kan-ta-kwana kan a mayar da wutar, bangarorin da abin ya shafa sun dauki haramar magance matsalar

A wata hira da ya yi da kafar labarai ta DCL Hausa, mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkar yada labarai AbdulAziz AbdulAziz ya bayyana yanda ministan harkokin wutar lantarki ya katse wata ziyarar aiki da yake yi a kasashen waje don amsa kiran shugaban kasa kan ya dawo gida ya dauki aikin gyaran wutar rigi-rigi.

Shi ma Mai bai wa Kasa shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu tuni ya dukufa, kan umarnin gaugawa da Shugaba Tinubu ya ba shi na samar wa Injiniyoyin gyaran wutan tsaro, inda akan haka ne a yau babban Ministan Tsaron ya biyo sahun sauran wadanda abin ya shafa, wajen bai wa   Shugaban rundunar tsaron Kasa Manjo Janar Kiristofa Musa Umarnin ya gaggauta samar da tsaro ga yankin Shiroro-Kaduna, inda tashoshin da ke bai wa Arewa  harsken lantarki mafi tsoka.

Idan dai ba a manta ba, yankin na Arewa ya shiga duhu na kusan sati biyu sakamakon lalacewar babbar tashar samar da wutar lantarki ga yankin wanda ake zargin ‘yan ta’adda ne suka ragargaza ta. Lamarin da ya janyo durkushewar kasuwanci, kiwon lafiya, da kuma walwalar jama’a a jihohi tara da abin ya shafa

A yanzu da Jami’an tsaro suka fara yi wa yankin kawanya, ana sa ran dawowar wutar kasa da sati daya inji kakakin fadar shugaban kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara