Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kama Habu Dogo, kasurgumin dan bindigar da ake nema ruwa jallo

-

 

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta sanar da nasarar kama wani kasurgumin dan ta’adda mai suna Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Habu Dogo a Sokoto da karin wasu kwamandojin kungiyar ‘yan a ware ta IPOB a kudu maso Gabas.

Daraktan yada labaran hedikwatar tsaron Manjo Janar Edward Buba a cikin wata sanarwa, ya ce an yi nasarar kama Habu Dogo ne a kauyen Rumji na karamar hukumar Illela ta jihar Sokoto.

A cewarsa, Habu Dogo na cikin jerin ‘yan bindigar da jami’an tsaro ke nema ruwa jallo a Nijeriya da ma makwabciya jamhuriyar Nijar saboda yanayi n ayyukan ta’addancinsa.

Su kuwa kwamandojin kungiyar ‘yan a waren ta IPOB da sojojin suka yi nasarar kamawa sun hada da Dr Nnamdi Chukwudoze da Chigozie Ezetoha da aka fi sani da Chapet da aka kama su a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Sauran su ne Mrs Ngozi Chukwuka da Mr Oyekachi Ohia da aka kama a karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara