Gamayyar kungiyoyin jami’iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta yi jinjina ga salon jagorancin Shugaban jami’iyyar APC na kasa na Abdullahi Umar Ganduje.
Kungiyar ta ce Ganduje na nuna kwarewa wajen tafiyar da jami’iyyar a matakin kasa musamman ganin yadda ya kwamitin yakin neman zaben Gwamnan jihar Ondo mai zuwa.
Shugaban kungiyar a wani taron manema labarai a Jos babban birnin jihar Plateau, Hon Saleh Abdullahi Zazzaga ya ce abin a yaba ne ganin yadda Ganduje da sauran shugabancin APC ya jawo wasu ‘ya’yan kungiyar da ma karin wasu bangarori domin tafiya tare da su a harkokin jami’iyyar.
A ranar 28 ga watan Oktoba, Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin mutane 305 da za su ba da gudunmuwa don tunkarar zaben Gwamnan jihar Ondo. Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu me ke jagorantar kwamitin. Kazalika, Gwamnan Ogun Dapo Abiodun ne shugaban kwamitin kula da harkokin kudi, yayin da Sanata Godswill Akpabio ne mataimakinsa.
Bugu da kari, akwai Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da Ministan yada labarai Mohammed Idris a matsayin Shugaba da mataimakinsa a kwamitin yada labarai.
Saleh Abdullahi Zazzaga ya ce wannan ya nuna karara yadda Abdullahi Ganduje ya himmatu wajen ganin an hada kan ‘ya’yan Jami’iyyar a mataki daban-daban.
Ya ma bukaci Ganduje da ya cigaba da tafiya da kowa da kowa domin ba kowa damar ba da tashi gudunmuwa don jami’iyyar ta cigaba.