Jami’an tsaro sun kwato mutane 19 da aka yi garkuwa da su a jihar Neja

-

Police

Rundunar ‘yan sanda ta ceto mutane 19 da aka yi garkuwa da su a dajin Gidan-Kwakwa da ke kan hanyar Tegina zuwa Zungeru a jihar Neja.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna ranar Talata.

 Ya ce, A ranar 1 ga watan nan da muke ciki aka samu labarin cewa a daidai wannan rana da misalin karfe 2:30,wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki kan wata mota da ta taho daga jihar Sokoto da ke kan hanyar zuwa Bayelsa a Gidan-Kwakwa da ke kan hanyar Tegina zuwa Zungereru inda suka yi awon gaba da mutane goma sha tara cikin dajin.

Ya ce da samun labarin, hukumomi sun aika da wata tawagar tsaro ta hadin gwiwa domin gano masu garkuwa da mutanen.

A cewar Abiodun masu garkuwa da mutanen sun zubar da mutane 12 da suka yi garkuwa da su bisa matsawar jami’an rundunar tsaro inda da ta ceto su da safiyar Asabar a dajin Pangugari da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Ya ce daga baya da misalin karfe 9 na dare, a wannan rana an ceto sauran mutane bakwai da aka yi garkuwa da su ba tare da jin rauni ba a dajin.

An kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa wani asibiti da ke kusa don kula da lafiyarsu kuma an sallame su don komawa jihar Sokoto a ranar 3 ga Nuwamba, 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara