DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya ta raba biliyan 45b ga jihohin kasar domin karfafa cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko 8,000-Farfesa Pate

-

Ministan Lafiya Farfesa Pate

Ministan lafiya da walwalar al’umma Farfesa Ali Pate ya ce gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 45 ga jihohi domin karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin wani taron hadin gwiwa na shekara ta 2024 da akai a Abuja.

Ya ce Naira biliyan 45 da aka raba wa cibiyoyin kiwon lafiyar zai shafi al’umma kai tsaye, inda ya kara da cewa sama da cibiyoyin dubu 8,000 suka amfana da kudade tare da kayan aiki domin ci gaba da duba marasa lafiya.

Farfesa Pate ya ce sama da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko 2,600 ana gab da farfado da su, kuma ana da shirin bunkasa wasu  ƙarin 2,000. Ministan ya bayyana kokarin ma’aikatar lafiya, inda ya bayar da rahoton cewa sama da ma’aikatan ta 40,000 ne aka horas da su, wanda aka yi niyyar su kai 120,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara