DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gyaran tsarin haraji: Kamata ya yi Tinubu ya hada kan ‘yan Nijeriya bawai raba wa ba – Bala Mohammed

-

Gwamnan Bauchi Bala Muhammed

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba kudirin gyara harajin da aka tsara kwanan nan, inda ya bukaci a sake duba shi tare da mai da hankali kan hadin kai ga kasa.

Ya yi kira ga shugaban kasa da ya dakatar da ci gaban kudirin gyaran harajin tare da karbar shawarwari masu yawa don tabbatar da adalci da daidaito kafin a zartar da shi a matsayin doka.

Musamman yadda kudurin ya haifar da kakkausar suka daga gwamnonin Arewa da masu masarautun gargajiya.                Amma duk da hakan shugaban ya yi watsi da kiraye-kirayen janye kudirin.

A lokacin da yake hira da Sashen Hausa na BBC, Gwamna Bala ya yi gargadin cewa shirin sake fasalin harajin zai kara tabarbare tattalin arzikin da yawancin jihohin arewacin kasar ke fuskanta.

Gwamna Mohammed ya yi bayanin cewa jihohin arewa, wadanda da yawa daga cikinsu sun riga sun fuskanci kalubalen kudi, kuma za su kara samun tabarbarewar tattalin arziki sakamakon sabon tsarin harajin idan aka tabbatar da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin kasar na kan hanyar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 cikin shekaru goma masu zuwa. Kashim...

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da direba da fasinjoji a Katsina

Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau a Katsina. Jami’an sun yi artabu da ‘yan...

Mafi Shahara