DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ku kakkabe sabuwar kungiyar “Lakurawa” – Mukaddashin Babban Hafsan Soji

-

Mukaddashin babban hafsan sojojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya umurci dakarun soji da su murkushe sabuwar kungiyar yan ta’adda wadda ta bulla a jihohin Sakkwato da Kebbi mai suna Lakurawa. 

Olufemi ya bayar da wannan umurni ne a lokacin ziyarar da ya kai hedikwatar runduna ta 8 dake Sakkwato, kwanaki kadan bayan hedikwatar tsaro ta fitar da rahoton bayyanar sabuwar kungiyar. 

A yayin ziyarar da ya kai a karamar hukumar Tangaza, daya daga cikin kananan hukumomin da yan bindigar ke ta’adi, mukaddashin babban hafsan ya bukaci al’umma su baiwa jami’an tsaro bayanai domin samun nasara a yakin da suke da matsalar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara