Hatsarin mota ya yi sanadin rayuwar mutum 10 a Jigawa

-

 


Mutum 10 sun rasa rayukansu inda ɗaya ya tsira da rauni sakamakon wani hatsarin mota da ya faru a kauyen Yanfari na karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wani bayani da ya fitar.

A cewar sa, wata mota ce kirar Toyota bus ta fada a kan wata Tirela dake ajiye.

DSP Lawan ya ce direban motar da mutum tara sun riga mu gidan gaskiya, yayin da mutun daya ya tsira da rauni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara