Gwamnatin Nijeriya ta samu lamunin karbo bashin dala miliyan 134 daga bankin raya Afirka

-

 

Gwamnatin Nijeriya ta samu lamunin karbo bashin dala miliyan 134 daga bankin raya Afirka 

Gwamnatin Nijeriya ta samu lamuni domin ciyo bashin da ya kai dala miliyan 134 daga bankin raya Afirka domin bunkasa fannin noma ta hanyar samar da iri da hatsi ga manoma a kasar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na ma’aikatar noma da samar da abinci, Anthonia Eremah ta fitar a Abuja, kamar yadda jaridar Daily Nigeria ta rawaito.

Ministan ma’aikatar Abubakar Kyari wanda ya bayyana haka a yayin kaddamar da noman rani na shekarar 2024/2025 a Calaba babban birnin jihar Cross River, ya ce bashin zai taimaka matuka wajen samar da abinci a kasar.

Ya kara da cewa tuni gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanya dokar ta-baci kan samar da

abinci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara