DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Na san wadanda suka sa hukumar EFCC mai yaki da cin hanci ta yi bincikena in ji wanda ya yi wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban kasa, Okowa

-

Tsohon Gwamnan jihar Delta Dr. Ifeanyi Okowa, ya ce ba ya jin tsoron binciken da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ke yi masa, saboda ya san mutanen da ke da hannu a binciken.
Okowa wanda shi ne tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekara ta 2023, ya ce dukkanin zarge-zargen da ake masa saboda siyasa ne.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ga shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Delta Manjo Janar Felix Mujakperuo mai ritaya, a gidan sa da ke birnin Asaba na jihar.
Hukumar EFCC na gudanar da binciken tsohon gwamnan akan zargin karkatar da kudaden da suka kai naira tiriliyan 1.3

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin buhun shinkafar waje mai nauyin 50KG ya koma N58,000 a wasu sassan Nijeriya in ji wani rahoton da majiyar DCL Hausa ta Punch ta wallafa.

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya,...

‘Yan siyasar da ke neman mukamai ba don talakawa suke yi ba – Zargin Bafarawa ga ‘yan siyasar Nijeriya

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya. Bafarawa, wanda ya kasance jigo...

Mafi Shahara