HomeUncategorizedZa mu shirya wa Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya zanga-zanga idan bai gyara...

Za mu shirya wa Sakataren Gwamnatin Tarayyar Nijeriya zanga-zanga idan bai gyara lamurransa ba – Magoya bayan APC

-

Gamayyar kungiyoyin da ke goyon bayan jam’iyyar APC a Arewa ta tsakiyar Nijeriya ta bukaci sakataren gwamnatin tarayya George Akume da ya hada kan jam’iyyar da shugabannin jam’iyyar a yankin Arewa ta tsakiya.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugabanta Hon Saleh Abdullahi Zazzaga, bayan taron kungiyar a Abuja, ta kuma yi kira ga sakataren Gwamnatin tarayyar da ya tsaya a matsayin shugaban jam’iyyar a shiyyar Arewa ta tsakiya ta hanyar tabbatar da cewa al’ummar yankin Arewa ta tsakiya sun mori irin salon mulkin Shugaba Tinubu.
Kungiyar ta yi gargadin cewa za ta shirya zanga-zangar adawa da sakataren gwamnatin tarayya idan ya kasa daukar matakan gaggawa don gyara rashin daidaiton nade-naden nasa, da kuma magance kura-kurai a tsarin shugabancinsa.
A cewar kungiyar, Mr George Akume ya kamata ya dauki dukkan shiyyar Arewa ta Tsakiya a nade-naden mukamai da ofishin sa ya yi.
Hon Saleh Abdullahi Zazzaga ya bayyana cewa yankin Arewa ta Tsakiya bai ci gajiyar mukaman da George Akume ya nada ba.
Sanarwar ta tunasar da sakataren gwamnatin cewa ya ci albarkacin yankin Arewa ta tsakiya ne aka nada shi mukamin, amma ya buge da nada ‘yan’uwansa ‘yan kabilar Tiv kadai a mukaman da yake badawa a ofishinsa.
Saleh Zazzaga ya yi kira ga Sanata George Akume da ya gyara wannan abin da suka kira barna, ko kuma su shirya masa zanga-zanga don nuna fushinsu a kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img