DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Matawalle ya isa birnin Riyadh na Saudiyya wajen babban taron tsaro na kungiyar IMCTC

-

 


Ministan kasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya Bello Matawalle ya isa birnin Riyadh na Saudiyya inda zai gana da Yariman kasar Mohammed bin Salman, a wani bangare na halatar taron kungiyar kasashen Musulmai da ke yaki da ‘yan ta’adda , IMCTC.

A yayin ziyarar aikin ministan ke yi a Saudiyya ya ziyarci hedikwatar kawancen kasashen Musulmi domin yaki da ta’addanci, inda ya yi godiya ga Sakatare Janar na kungiyar ta IMCTC, bisa gudunmuwar da suke bai wa Nijeriya ta hanyar horas da sojojinta dubarun yaki da ta’addanci.






LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara