DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Buhun shinkafar waje ya doshi naira dubu 100 a sassan Nijeriya

-

Farashin buhun masara na neman zama gagara badau musamman ga masu karamin karfi a kasuwar Mile 12 International Market Legas a kudancin Nijeriya, inda a makon nan ake sayar da buhun tsohuwar masara N100,000 cif, yayinda ita kuwa sabuwar ake saidawa N90,000, sai dai a makon jiya N95000 aka sai da buhun tsohuwar masara, sai kuma sabuwar aka sai da N75000 a makon da ya wuce.
To a kasuwar Dawanau jihar Kano, N64000 ake sayar da buhun masara a satin nan mai ƙarewa.
A wannan mako farashin masara bai sauya ba a kasuwannin jihar Adamawa, ta na nan a kan N67000, yadda aka saida a makon daya shude.
Hakazalika, a kasuwar Mai’adua jihar Katsina, N70,000 daidai aka sai da buhun masara a makon jiya, to a makon nan ma haka ake saidawa.
A kasuwar Dandume jihar Katsinan N57000- 65000 ake sai da buhun masara a satin nan.
Da DCL HAUSA ta leka kasuwar Giwa jihar Kaduna kuwa, ta taras cewa an samu ragin N4000 kan farashin buhun masara na makon jiya da aka saya N68000, a makon nan kuwa ake saidawa N64000.
Masarar tafi sauki a kasuwar Saminaka jihar Kadunan da ake saidawa N54000-55000 a satin nan, amma haka farashin yake a makon daya gabata.
Ita kuwa Shinkafar Hausa tafi sauki a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da ake saidawa N137-138,000 a satin nan, amma a makon daya shude N135000 aka sai da buhun.
A kasuwannin jihar Adamawa N140-145000 ake sayar da buhun shinkafa ‘Yar gida a satinnan, bayan da a makon jiya aka sai da N138,000.
N150,000 ake sayar da buhun shinkafa ‘Yar gida a kasuwannin jihohin Kano da Legas a satin nan, sai dai farashin ya bambanta a makon jiya, inda a kasuwar Mile 12 International Market Legos aka sai da buhun N147000.
A kasuwar Giwa jihar Kaduna N155000 ake sai da shinkafar Hausa a satin nan,sai dai a makon jiya N140,000 aka sai da buhun, an samu karin N15000 kenan a mako ɗaya.
To a Dandume jihar Katsina N140,000-160,000 ake sai da buhun shinkafar Hausa a wannan satin, bayan da a makon jiya aka sai da N140-155000.
Sai kuma Saminaka jihar Kaduna ake sai da buhun shanshara na Shinkafa N49000-50,000, haka farashin yake a makon daya gabata. 
A bangaren Shinkafar waje kuwa, ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano inda ake saidawa N105,000 a wannan sati.
Sai kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa ake sayar da buhunta N90-95000 a makon nan, bayan da a makon jiya aka sai da N90000.
Sai kuma mu nausa kasuwar Giwa jihar Kaduna da ake sai buhun Shinkafar ‘yan gayu N90,000 a wannan sati, haka farashin yake a makonni biyu na watan Nuwamba na shekarar 2024.
To a kasuwar Mile 12 International Market, ana sayar da buhun shinkafar bature N85000, yayinda a makon daya wuce aka sai da N80,000, an samu karin N5000 kan farashin makon daya gabata.
Can a kasuwar Mai’adua jihar Katsina, an sai da buhun shinkafa ‘yar gwamnati kan kuɗi N83000 a makon daya gabata, sai a makon nan ake saidawa N84000.
Sai dai, a kasuwar Dandume jihar Katsinan, N75000 ake sai da buhunta a satin nan, haka nan aka sai da makon daya shude.
Yanzu kuwa sai mu leka bangaren Wake, ga masu cin garau-garau ko kosai ko dai alala a gyara zama don farashin wake na makon nan.
Farashin tsohon waken ya fadi a kasuwar Mile 12 International Market Legas a wannan mako da ake saidawa N220,000, bayan da a makon jiya aka sai da N260,000, sai dai farashin sabon bai sauya daga yadda aka sai da a makon jiya, N180,000.
A kasuwannin jihar Adamawa N125000-130,000 ake sai da buhun farin wake kanana a makon nan.
N120,000 ake sai da buhun wake a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan mako, haka nan aka sai da makon daya wuce.
An samu sauƙin N20,000 kan farashin wake a kasuwar Giwa jihar Kaduna da ake saidawa N140,000 a satin daya shuɗe, amma a wannan sati N120,000 ake sai da buhunsa.
A kasuwar Dandume jihar Katsina N90,000-140,000 ake sayar da buhun wake a satin nan da ke dab da ƙarewa.
Sai kuma mu ƙarƙare farashin wake da kasuwar Saminaka jihar Kaduna, inda ake sai da buhun kananan wake 110,115 – 120,000 a makon nan.
Taliyar Spaghetti tafi sauki a kasuwar Mai’adua jihar Katsina wanda ake sai da Kwalinta N19300 a makon nan, a makon jiya kuwa aka sai da N19200.
Sai dai a kasuwar zamani da ke jihar Adamawa farashin na nan kamar na makon jiya da aka sai da N19700.
An samu ragin N500 kan farashin Kwalin taliya a kasuwar Giwa jihar Kaduna da aka sai da N20,500 a makon daya wuce, sai a makon nan ake saidawa N20,000 cif, yayinda ita kuwa kasuwar Mile 12 International Market Legos aka samu karin ₦500 kan farashin makon jiya da aka sai da N20,000, sai kuma makon nan ake saidawa N20500.
Ita ma kasuwar Dawanau jihar Kano N20500 ake sai da kwalin taliya a wannan sati.
  
Taliyar tafi tsada a kasuwar Dandume jihar Katsina, wanda ake Saidawa N21,000.
Alkhaluman da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar na nuna cewar hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 33.88 a watan Oktoban 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara