Rikicin manoma da makiyaya a Nasarawa ya yi ajalin mutum 3

-

Akalla mutum uku ne suka rigamu gidan gaskiya, sakamakon wani sabon rikici da ya faru tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Toto jihar Nasarawa.
Kwamishinan yan sandan jihar Umar Nadada, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rikicin ya faru ne a wani gari mai suna Dogon Dutse da ke tsakanin kananan hukumomin Nasarawa da Toto.
Ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin ne ranar litinin da misalin karfe 4:30pm, bayan da jami’ai suka isa wurin sun tarar da mutum biyu sun mutu inda hudu suka samu raunukka.
A cewar kwamishinan, daga baya an gano gawar mutum daya a cikin daji kuma yanzu haka suna gudanar da bincike domin gano musabbabin rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara