HomeUncategorized'Yan Nijeriya sun shirya kayar da Tinubu zabe a 2027 saboda tsadar...

‘Yan Nijeriya sun shirya kayar da Tinubu zabe a 2027 saboda tsadar rayuwa in ji Bode George

-

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa Cif Bode George ya ce ‘yan Nijeriya na shirin juyawa gwamnatin Tinubu ta jam’iyyar APC baya a zaben shekara ta 2027 da ke tafe.
Bode George wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai don bikin cikarsa shekaru 79, ya yi fatar cewa PDP za ta nutsu don dinke duk wata baraka da ke ciki don ceto ‘yan Nijeriya daga mulkin APC. 
Ya bayyana rashin jin dadi akan yadda wasu marar kishi a jam’iyyar su ka hada kai da APC wajen yi wa PDP makarkashiya a zaben 2027, inda ya ce dole a taka musu burki.
George, ya nuna cewa PDP ce kawai za ta iya ceton ‘yan Nijeriya daga halin da su ke ciki, amma dole sai sun hada kai za su cimma hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img