DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za mu sake gabatar da kudurin wa’adin shekaru shida ga shugaban kasa da gwamnoni, inji dan majalisar da ya kawo kudurin, Ikenga Ugochinyere

-

Dan majalisar wakilan Nijeriya da ke jagorantar gabatar da kudurin kara wa’adin shugaban kasa da gwamnoni Ikenga Ugochinyere (PDP, Imo) ya ce za su sake gabatar da kudurin wanda majalisa ta ki amincewa da shi a zamanta na ranar Alhamis.
Wannan kudurin, ko baya ga neman kara wa’adin zuwa shekara shida, na son a gudanar da zabe a matakin kasa da jihohi a rana daya tare da yin tsarin karba-karba na shugabanci tsakanin yankin arewa da kudancin Nijeriya.
Sai dai bayan sake gabatar da kudurin karo na biyu, ‘yan majalisar sun yi watsi da shi ba tare da bada damar tattaunawa a kai ba.
Duk da haka, dan majalisar Ugochinyere, a cikin wani bayani da ya fitar, ya sha alwashin sake gabatar da kudurin bayan yin tuntuba domin ganin cewa sun yi nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin buhun shinkafar waje mai nauyin 50KG ya koma N58,000 a wasu sassan Nijeriya in ji wani rahoton da majiyar DCL Hausa ta Punch ta wallafa.

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya,...

‘Yan siyasar da ke neman mukamai ba don talakawa suke yi ba – Zargin Bafarawa ga ‘yan siyasar Nijeriya

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya. Bafarawa, wanda ya kasance jigo...

Mafi Shahara