DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a kammala gyaran matatar man Kaduna zuwa karshen Disamba 2024

-

Manajan daraktan matatar mai ta Kaduna Dr. Mustafa Sugungun ya ce ana sa ran kammala gyaran da ake yiwa matatar Kaduna zuwa karshen shekararnan ta 2024.

Kamfanin mai na kasa NNPCL ne ya bayar da kwangilar gyaran wani bangare na na matatar mai ta Kaduna ga kamfanin kasar Koriya ta Kudu ‘Daewoo Engineering & Construction’ akan kuÉ—i dala miliyan 741.

Bayan kammala gyaran, matatar wadda ke aka gina domin tace ganga 110,000, za ta rika tace kashi sittin na gangar mai 66,00 a kowace rana.

A jawabinsa, babban manajan wanda ya samu wakilcin manajan sashen ayyuka na matatar Mista Emmanuel Ajiboye, a wurin kaddamar da aikin gyaran wata makaranta da kamfanin ya yi, ya ce idan aka kammala gyaran matatar za ta samar da ayyukan yi, bunĆ™asa kasuwanci da kananan sana’o’i a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara