An kama wani mutum da ake zargi yaudarar mutane a matsayin dan’uwa ga Sheikh Gadon Kaya a jihar Kano

-

Jami’an ‘yan sandan Kano sun kama wani mutum da ake zargi da yaudarar mutane ta hanyar tura musu sakon kudi na bogi.
Ana kuma zargin mutumin mai suna Sunusi Aminu dake Kofar Nassarawa, da yin karyar cewa shi dan uwan sanannen malamin addinin musuluncinnan ne Sheikh Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya domin samun yardar mutane a lokacin da suke kasuwanci, daga baya sai ya yaudaresu da sakon kudi na bogi a matsayin ya tura a asusun banki.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce sama da mutane 20 sun gabatar da korafi akan mutumin bayan kama shi kuma ana zargin ya karbi kayan da suka kai naira miliyan 2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara