Gwamnatin Nijeriya ta samu nasarar janyo dala biliyan 1.27 daga masu saka hannun jari na Kasashe mambobin BRICS

-

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Nijeriya ta samu nasarar janyo masu zuba hannun jari daga kasashen BRICS wadanda suka zuba jarin dala biliyan 1.27 a watan Yunin 2024 wanda yasa hannun jarin kasashen waje ya karu daga dala miliyan 438.72 da aka samu a shekarar 2023.
Kungiyar kasashen BRICS da tattalin arzikinsu ke bunkasa wacce kuma ke neman zama kishiya ga kasashen Yamma sun hada da Brazil, Russia, India, China, South Africa, da kuma Iran, 
Akwai kuma kashe irin su Egypt, Ethiopia, da ma Hadaddiyar Daular Larabawa dukkanin su cikin ƙungiyar ta BRICS
Da yake jawabi a wurin taron dandalin bankunan nahiyar Afirka da ƙasar China, Kashim Shettima wanda ya samu wakilcin mai baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka Dr Aliyu Modibbo, ya ce alaƙar Nijeriya da Kasashen BRICS na kara karfi musamman wajen bunkasa tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara