HomeUncategorizedDan majalisar tarayya na Katsina ya share wa al'ummarsa hawaye, bayan gina...

Dan majalisar tarayya na Katsina ya share wa al’ummarsa hawaye, bayan gina musu titin da suka jima suna rokon a gina musu

-

Dan majalisar tarayya da ke wakiltar karamar hukumar Katsina a majalisar wakilai ta tarayya, Hon Sani Aliyu Danlami ya share wa wasu al’ummar cikin kwaryar birnin Katsina hawaye, a wani aikin titin da suka jima suna rokon a yi musu, amma abin ya ci tura.
Titin da dan majalisar ya gyara shi ne wanda ya tashi daga Masallacin Juma’a na GRA ya bi ta Gidan Dawa ta zarce zuwa makabarta har ta bulle zuwa titin Ring Road na Liyafa.
Kasa da wata daya dai dan majalisar tarayyar Sani Aliyu DanLami ya kaddamar da aikin, amma har an kammala shi.
Aikin dai, na daga cikin ayyuka uku na tituna da dan majalisar tarayya Hon Sani Aliyu DanLami yake gudanarwa a halin yanzu a karamar hukumar Katsina, inda yake wakilta.
Sauran ayyukan hanyar sun hada da wadda tashi daga bayan gidan gwamnati a Modoji sai wadda ta bi ta bayan Customs Base a cikin GRA da kuma Layout akan titin Dr Garba Shehu Matazu.
Ayyukan na daga cikin kokarin da Sani Aliyu DanLami yake yi na inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img