DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar direbobi masu dakon kaya ta Nijeriya ta koka kan karbar haraji ba bisa ka’ida ba a jihar Kogi

-

Kungiyar direbobi masu dakon kaya ta Najeriya HDHTAN reshen jihar Kogi, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta ba da goyon baya don kawo karshen karbar haraji daga mambobinta ba bisa ka’idaba. 
Shugaban kungiyar ta HDHTAN reshen jihar Kogi, Trust Chukwuma, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin taron manema labarai da ya kira a Lokoja, inda ya bayyana nasarorin da kungiyar ta samu daga kafuwarta, da suka hada hana aikata miyagun ayyuka ta hanyar amfani da manyan motoci. 
Ya kuma ce wannan kokarin ya taimaka wajen sanya ido kan yadda ake amfani da manyan motoci ana aikata miyagun laufuka, da kuma bada rahoton laifukan ta’addanci, kamar garkuwa da mutane, da safarar mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara