DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci Shugaba Tinubu ya biya matasan da suka yi shirin N-Power hakkokinsu cikin sa’o’i 72

-

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya umarci ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, kan ya tabbatar da cewa an bude dukkanin asusun hukumar kula da harkokin bayar da tallafi ta kasa (NSIPA) da aka rufe a baya, cikin sa’o’i 72, domin samun damar gudanar da shirye-shiryen hukumar yadda ya kamata. 
Majalisar ta kuma bukaci ministan ya tabbatar an tura kudade ga hukumar ta NSIPA domin biyan bashin alawus-alawus na matasa dubu 395 da 731 da suka yi shirin N-Power a fadin kasar, ba tare da bata lokaci ba.
Kazalika majalisar ta bukaci Ministan jin kai da kare aukuwar bala’u, Nentawe Yilwatda, da ya tabbatar da an magance matsalolin da ke kawo cikas ga duk wani shiri karkashin hukumar ta NSIPA cikin sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara