Shugaba Tinubu ya ba da umurnin aiki kan korafe-korafen da ‘yan arewa ke yi kan dokar haraji

-

Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya umurci ma’aikatar shari’a da majalisar dokokin kasar su magance korafe-korafen da suka taso dangane da kudirin dokar haraji.
Tun bayan gabatar da wannan kudurin na garambawul ga dokar haraji gwamnatin Tinubu ke shan suka, lamarin da ya sa gwamnonin arewa su ka juyawa Tinubu baya tare da yin watsi da wannan dokar.
Gwamnonin sun yi zargin cewa dokar za ta baiwa wasu jihohin fifiko tare da mayar da yankin arewa baya.
Sai dai ministan yada labarai Mohammed Idris ya ce shugaban kasa ya ji korafe-korafen da ‘yan Ć™asar ke yi kuma ya umurci majalisa da ma’aikatar shari’a da sauran masu ruwa da tsaki su yi aiki tare don gyara dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara