A karon farko farashin Bitcoin, ya haura dala dubu 100 a dandalin hada-hadarsa wato Bitstamp.
Bitcoin dai, shi ne kudin Crypto mafi tsufa da daraja kuma sananne, fiye da sa’o’i 24 ya karu da kusan kashi 4 da digo 8, inda ya kai dala dubu 103 da 252 da misalin karfe 3 na asubahi agogon GMT.
Dama dai cikin kwanaki bakwai da suka gabata, manyan kudaden crypto sun samu tagomashi da fiye da kashi 7 cikin 100.
Yanzu haka dai duk Bitcoin daya ya kai Naira Miliyan 168 da 212 da 686.