DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin wake da taliya ya sauka a wasu kasuwannin Nijeriya

-

Shinkafar waje ta kusa kullewa dubu 100 a kasuwar Giwa jihar Kaduna, inda ake sayar da ita 99,000, 
A kasuwar Mai’adua jihar Katsina naira 97,000 ne kudin buhun shinkafar waje a satin nan, an samu karin naira 9,000 kan yadda aka saida a makon da ya shude   88,000.
Sai dai farashin bai karu ba a kasuwar Dandume da ke jihar Katsina a makon nan, da ake saidawa  N85000 haka aka saida tun a makon da ya gabata.
N85,000 – 90,000 ake sayarda buhun shinkafar waje a kasuwannin jihar Adamawa a wannan mako, banbancin kadan ne da na satin da ya wuce da aka saya 
N87,000 – 90,000.
A kasuwar Mile 12 International an samu karin dubu uku kan buhun shinkafar waje inda ake saida ita 90,000, sabanin 87,000 da aka saida a makon da ya gabata.
SHINKAFAR HAUSA
Shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwannin jihar Adamawa, N160,000 ake sayarda buhu a wannan makon, inda a makon jiya take N140,000 zuwa 145,000.
A wannan makon ₦155,000 ake sayarda shinkafar Hausa a kasuwar Giwa jihar Kaduna da kasuwar Mile 12 International Market, haka farashin yake a makon jiya.
A kasuwar Mai’adua jihar Katsina farashin shinkafar ya kai naira N140,000 zuwa 145,000 inda a makon da ya shude aka saida N138,000.
A Can  kasuwar Dandume, mako na biyu kenan farashin bai sauya ba, ₦140,000 zuwa ₦160,000 ake sayar da shinkafar hausa a kasuwar. 
Shinkafa Shanshera kuwa  N55,000 zuwa N58,000 ake saidawa a kasuwar Saminaka jihar Kaduna a makon nan, a makon da ya shude kuwa  N50,000-55,000 ake sai da buhunta.
WAKE
Farashin wake ya kara saukowa a kasuwar Mile 12 International inda ake sayarda tsohon wake naira 200,000 sabanin 210,000 da aka sayarda buhun a baya, sabon wake kuwa naira N180,000 .
A kasuwannin jihar Adamawa farashin wake ya yi tashin gwauron zabi, a wannan mako N155,000 zuwa 160000 ake sayarda buhun manyan wake, sai dai a makon da ya shude N120,000 aka saida buhun kananan wake  a kasuwar. 
A kasuwar Dandume  jihar  Katsina  ₦90,000 zuwa ₦115,000 ake sayarda buhun kananan wake a makon nan, a satin da ya gabata  N90,000-140,000 aka sai da.
Naira 120,000 ake sayarda buhun wake a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan mako.
Farashin bai sauya zani ba a kasuwar  Saminaka  jihar  Kaduna, wanda ake sai da buhun wake N110,000-120,000 sati biyu da suka gabata
Amma a kasuwar Giwa jihar Kaduna an samu saukin N10,000, inda a makon nan ₦105,000 ake saida buhu, a satin da ya shude  kuwa  N115,000 aka sai da buhun wake.
MASARA
Farashin masara a kasuwar Mai’adua ya sauka daga naira 69,000 a makon da ya shude zuwa naira 66,000 – 67,000 a wannan mako, haka farashin yake a kasuwannin jihar Adamawa.
Ana sayar da buhun masara  ₦50,000 zuwa ₦60,000 a kasuwar Dandume jihar Katsina a satin nan, haka farashin yake a makon jiya.
N60,000 ake sayar da masara a kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon nan, yayinda a makon jiya aka sai da N64,000, an samu sauƙin Naira 4000 kenan.
Can ma a Saminaka farashin ya sauka, inda ake sayar da masarar Naira 52,000 – 55,000 a wannan mako, a makon jiya kuwa N55,000 zuwa 57,000 aka saida.
A kasuwar Mile 12 farashin tsohuwar masara ya sauka inda ake sayar da buhunta 95,000 a wannan makon, yayinda a makon da ya wuce aka saidai 105,000, an samu sauƙin 10,000 kenan a satin nan.
Farashin sabuwar masara bai sauya ba yana nan N90,000 a kasuwar Mile 12.
TALIYA
Bari mu karkare da farashin kayan abincin da  taliya, wadda ke ci gaba da yin sauki a kasuwannin Nijeriya.
A wannan makon ana sayar da kwalin taliya N20,000 a kasuwar Dandume  jihar Katsina, yayinda a satin da wuce aka saida 22,000.
19,500 taliya take a Kasuwar Giwa jihar Kaduna a makon nan, sai makon da ya shude aka  saida  N20,000.
Farashin bai sauya ba a kasuwar Mile 12 International da ke Lagos wanda aka saida  N21,000 hakama a jihar Adamawa farashin yana nan kan N19700 da aka saida a makon da ya gabata. 
To a kasuwar  Mai’adua  jihar Katsina  N18000 ake saida kwalin taliyar Spaghetti  a makon nan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara