An kusa kammala gyaran matatar mai ta Fatakwal ta biyu – fadar gwamnatin Nijeriya

-

Fadar gwamnatin Nijeriya ta ce matatar mai ta Fatakwal ta biyu, mai karfin tace ganga 150,000 na danyen mai a kowace rana za ta soma aiki nan bada jimabawa ba.
A kwanakinnan ne matatar Fatakwal dake tace ganga 60,000 rana ta soma aiki yayinda ake ci gaba da gyaran dayar matatar wadda ta fi girma.
Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi watsi da kalamai marasa kyau da ake yadawa kan sabuwar matatar da ta fara aiki.
Duk da cewa matatar ba ta aiki kashi 100, amma kashi saba’in yana aiki yadda ya kamata, inji Bayo Onanuga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara