Babban sufetan ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ya ce bangaren shari’a na kasar nan ya yi rauni kuma yana bukatar sauye-sauye.
Ya kuma yi kira da ‘yan Nijeriya su daina zargin ‘yan sanda da zama matsala a kasar.
Babban Sufetan wanda ya samu wakilcin mai magana da yawun rundunar ACP, Muyiwa Adejobi a wurin taron kungiyar masu dauko labarin miyagu laifukka, ya ce ba ‘yan sanda ne kawai bangaren doka na kasar dake fuskantar matsaloli ba, sai dai suna kokarin gyara tsarin.