Nijeriya ta musanta yunkurin shigowa da sojojin Faransa ko ba ta damar hakar ma’adanai

-

Fadar gwamanatin Nijeriya ta musanta yunkurin mikawa kasar Faransa bangaren hako ma’adanai ko shigowa da sojojin kasar kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta.
A lokacin ziyarar da ya kai Faransa a kwanannan, Shugaba Bola Tinubu da Emmanuel Macron sun sanya hannu kan yarjejeniyar aiki tare domin karfafa samar da ma’adai tsakanin kasashen biyu.
Sai dai yarjejeniyar ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke zargin Faransa za ta karbe bangaren hakar ma’adanai na Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Sunday Dare ya ce Faransa za ta taimakawa Nijeriya ne kawai ta bangaren bincike da kuma hosasda dalibbai akan albarkatun ma’adanai na kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara