DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Masu Neman takarar shugabancin Nijeriya daga Arewa a 2027 su jira sai 2031 bayan Shugaba Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu – George Akume

-

Sanata George Akume

Sakataren gwamnatin Nijeriya Sanata George Akume ya ce manyan ‘yan siyasar Arewacin Nijeriya su yi hakuri har sai Shugaba Tinubu ya kammala wa’adi na biyu na mulkin kasar kafin su fara nema.

Ya ma kama sunan Atiku Abubakar, inda ya ce, daina tunanin zai zama shugaban kasa a 2027.
George Akume wanda ya yi magana a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na TVC kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, ya ce Kudancin Nijeriya ne ke da alhakin samar da shugaban kasa a shekarar 2027.
Ya ma yi nasiha ga Atiku Abubakar na PDP cewa idan Allah Ya so zai zamo shugaban kasa, ko ya shekara 90 a duniya zai iya zama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara