DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta yi watsi da bukatar bada belin tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello

-

Yahaya Bello

Babbar kotun tarayya da ke Maitama a babban birnin Nijeriya Abuja, ta yi watsi da bukatar bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello. 

Google search engine

Da ta ke yanke hukunci a zaman kotun na ranar Talata mai shari’a Maryanne Anenih, ta yi zargin rashin cancantar neman belin na Yahaya Bello.

Tun da farko, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Nijeriya EFCC ce, ta gurfanar da Yahaya Bello, tare da wasu mutane biyu a gaban kotun, bisa tuhumar su da karkatar da makudan kudade da yawansu ya kai Naira biliyan 110.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An gudanar da addu’o’in neman tsari daga hare-haren ‘yan bindiga a jihar Neja

Mazauna yankin jihar Neja ta Arewa sun gudanar da addu’o’i na musamman a filin Idi da ke Kontagora, hedkwatar karamar hukumar Kontagora, domin neman taimakon...

‘Yan siyasa a Nijeriya sun fi maida hanakali kan siyasa maimakon magance matsalolin al’umma – Sarkin Onitsha

Sarkin Onitsha, Igwe Nnaemeka Achebe, ya caccaki ‘yan siyasa bisa mayar da hankali kan siyasa maimakon gudanar da mulki yadda ya kamata tun kafin zaben...

Mafi Shahara