DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An kama masu kai wa barayin daji ‘uniform’ din sojoji a jihar Katsina

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da safarar ‘uniform’ na sojoji zuwa ga barayin daji a jihar.
A cikin wata sanarwa daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sadiq Aliyu Abubakar da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce kan titin Yantumaki-Kankara, ne jami’ansu suka yi nasarar kama wani matashi mai suna Aminu Hassan na yankin Dandubus cikin karamar Danja dan shekaru 25 dauke da kayan sojoji kala biyu a cikin leda baka.
Sanarwar ta ce da aka tsananta bincike ne aka kuma kamo karin wasu mutane uku da ake zargi da suka hada da Lawal M Ahmad dan shekaru 29 da Isma’il Dalhatu mai shekaru 24 dukkaninsu da ke Basawa, Zaria jihar Kaduna, sai Shafiu Adamu mai shekaru 28 da karamar hukumar Soba jihar Kaduna.
‘Yan sandan sun ce an gano karin kayan wato ‘uniform’ na sojoji kala 14 da na ‘yan sanda kala daya daga hannun waÉ—anda ake zargin wlda ake kyautata zaton za su kai wa barayin daji ne.
ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce a lokacin da ake yi wa waÉ—anda ake zargin tambayoyi, sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa, kuma za a gurfanar da su gaban kotu don fuskantar shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara