HomeLabaraiEFCC ta dakume wasu da ake zargi masu damfara ta Internet ne...

EFCC ta dakume wasu da ake zargi masu damfara ta Internet ne su 23 a Jihar Oyo

-

Mutane 23 da EFCC ta kama bisa zargin damfara ta intanet 

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC ta kama wasu mutane 23 da ake zargi da yin damfara ta intanet a yankin Akobo da ke Ibadan a jihar Oyo. 

Jami’an hukumar ta EFCC shiyyar Ibadan ne suka kama wadanda ake zargin, biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu. 

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba a shafinta na X, ta ce yayin samamen jami’an sun kuma kwato wasu kayayyaki da ake kyautata zaton an siye su da kudaden haramun ne. 

Kayayyakin da suka hada da manyan motoci na alfarma guda takwas da na’urori sai wayoyin hannu da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Sarkin Daura ya nada Hamza Sule Sarautar Sadaukin Kasar Hausa

Maimartaba Sarkin Daura Alh Faruk Umar Faruk ya nada Hon. Hamza Sulaiman Faskari Kwamishinan mahallin jihar katsina sarautar Sadaukin Kasar Hausa a fadarsa dake garin...

Kawance domin kayar da Tinubu a 2027 ba zai yi wani tasiri ba, bata lokaci ne kawai, in ji dan jam’iyyar PDP Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi watsi da gamayyar jam’iyyun adawa na siyasa da ake tattaunawa a kai, da nufin kifar da Gwamnatin...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa...

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana...

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a...

Most Popular

spot_img