DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sakataren gwamnatin Jihar Bauchi ya yi murabus daga mukaminsa

-

Sakataren gwamnatin Jihar Bauchi ya yi murabus

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir, ya amince da murabus din sakataren gwamnatin jihar Barista Ibrahim Kashim.

A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai Mukhtar M Gidado, ya fitar a ranar Juma’a, ta nuna cewa murabus din ya fara aiki nan take. 

Sanarwar, ta kuma umarci shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Dakta Aminu Hassan Gamawa, da ya rike mukamin a matsayin rikon kwarya ba tare da bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin buhun shinkafar waje mai nauyin 50KG ya koma N58,000 a wasu sassan Nijeriya in ji wani rahoton da majiyar DCL Hausa ta Punch ta wallafa.

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya,...

‘Yan siyasar da ke neman mukamai ba don talakawa suke yi ba – Zargin Bafarawa ga ‘yan siyasar Nijeriya

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya. Bafarawa, wanda ya kasance jigo...

Mafi Shahara