![]() |
Yan sandan Najeriya |
Rundunar yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar wani mutum da ba a bayyana sunansa ba, bayan da ya cinna musu wuta shi da matarsa, a yankin Ijoka ta ƙaramar hukumar Akure a Jihar.
A wata sanarwa da Rundunar yan sandan jihar ta wallafa a shafinta na X ranar Juma’a, ta ce ma’auratan sun shafe shekaru goma da yin aure kuma suna da yara biyu, kafin su rabu saboda wata matsala da ba a bayyana ba.
A cewar, yan sandan, mutumin ya dauki wannan danyen hukuncin ne bayan da matar taki amincewa su sasanta kan su, su ci gaba da rayuwa a matsayin ma’aurata.