Ba mu taba morar dimokradiyya ba irin zamanin Shugaba Tinubu tun 1999 – Wasu ‘yan Arewa ta tsakiyar Nijeriya

-

Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya sun ce amince Shugaba Tinubu ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a babban zaben 2027 da ke tafe.
A cikin wata sanarwa daga shugaban kungiyar gamayyar kungiyoyi magoya bayan jam’iyyar APC na yankin Hon Saleh Abdullahi Zazzaga, ta ce dalilin kungiyar na nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu saboda ya ba da damarmaki masu tarin yawa a yankin tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2023.
Yanke shawarar gamayyar kungiyoyin ya biyo bayan wasu kungiyoyin da suka fito suka fara nadamar zaben Shugaba Tinubu, har suke cewa a zabe na gaba, dan Arewa za su zaba a matsayin shugaban Nijeriya.
Sai dai, magoya bayan jam’iyyar APC na yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya sun ce sun ji, sun gani a sake zaben Shugaba Tinubu biyo bayan irin nau’ikan cigaban da ya kai musu a yankin na aikace-aikacen raya kasa, nade-naden mukamai da inganta tsaro.
Sanarwar ta ce Arewa ta tsakiyar Nijeriya ba ta morar dimokradiyya ba tun shekarar 1999 irin yadda take mora a halin yanzu karkashin Shugaba Tinubu.
Hon Saleh Abdullahi Zazzaga ya ce yankin na goyon bayan sake zaben Shugaba Tinubu a shekarar 2027 saboda tsare-tsaren cigaban da ya bullo da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara