An kakkaɓe Lakurawa a Najeriya – Ministan tsaro Bello Matawalle

-

 

Ministan kasa a ma’aikatar tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa an fatattaki Kungiyar lakurawa daga Nijeriya

Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa dake Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Ya uma yi watsi da maganar kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara Mohammed Shehu Dalijan, wanda ya yi zargin cewa ‘yan Kungiyar ta  Lakurawa ne ke da alhakin tada bama-baman da suka hallaka mutane da dama a jihar makonnin da suka gabata.

Kungiyar, wadda ta fara bulla a tsakanin shekarar 2016 ko 2017 a jihar Sakkwato, ta fara ne a matsayin kungiyar kare kai dake kare al’ummar da yan bindiga da suka addaba a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara