DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Matar hamɓararren shugaban kasar Siriya, Bashar Al’assad ta nemi takardar saki domin ta koma Burtaniya

-

 Matar hamɓararren shugaban kasar Siriya, Bashar Al’assad ta nemi takardar saki domin ta koma Burtaniya

Asma al-Assad, matar hambararren shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad  ta shigar da karar neman saki daga mijinta tare da neman komawa kasarta Burtaniya. 

Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito cewa Asma al-Assad ba ta jin dadin rayuwar gudun hijira da take yi tare da mijinta a birnin Moscow.

Ana dai zargin cewa Asma ta shigar da kara a gaban wata kotun kasar Rasha inda ta nemi izini ficewa daga kasar, yayin da mahukuntan kasar Rasha ke duba bukatarta, a cewar kafar yaɗa labarai ta NDTV.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya

An saka ranar da za a fitar da sakamakon binciken zargin alaka da muggan kwayoyi da ya hada da Shugaba Tinubu na Nijeriya. Ana dai...

Za mu iya cin zabenmu ko babu ku, kalaman Elrufa’i ga gwamnonin Nijeriya

  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa sabuwar kawancen jam’iyyu adawa na da karfin da zai kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu...

Mafi Shahara