Hanyoyin kare kai yayin aikin Hajji

-

1. Ku kasance cikin tsari: Ko yaushe ku rataya katin shaidarku tare da sauraron sanarwa, kuma ku bi umurnin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro don tabbatar da tsaro.

2. Takaita shiga cikin taron jama’a: Ku bi hanyoyin da aka kebe da kuma kiyaye lokutan da aka ware muku na zuwa ibada, musamman a lokacin jifan shaidan, don guje wa turmutsitsi, daukewar numfashi sakamakon zafi da kishirruwa.

3. Kishir- ruwa: Ku tabbatar kun sha ruwa sosai tare da kasancewa a inuwa don guje wa matsalolin da ka iya tasowa sakamakon zafin rana.

4. Kiyaye lafiyarku: Kowanne mahajjaci ya kamata ya san wuraren da cibiyoyin lafiya suke, waÉ—anda ke da wasu magunguna su rinka tafiya ko’ina da su, a rinka yin tsafta, sannan a lura da irin takalman da za a sanya yayin ibada don gudun jin raunuka.

5. Kiyaye ingancin abinci: Ku guji siyan abinci a kan tituna barkatai ko kuma wuraren da ba a tantance tsaftar su ba.

6. Kula da kayayyaki masu daraja: Ku rage yawo da kayayyakinku masu tsada don gudun faduwa ko sacewa.

7. Haramtattun kayayyaki: Haramun ne mahajjaci ya shiga jirgi da duk wani karfe ko wuka ko allura ko reza ko almakashi ko goro ko kuma duk wani nau’in kayan maye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara