Hukumar karbar korafe-korafe ta kama waɗanda ake zargi da badakalar filaye a Kano ciki har da jami’an tsaro

-

Hukumar karbar korafe-korafe ta Jihar Kano 

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano PCACC, ta kama waɗanda ke da hannu cikin almundahanar filaye, da suka hadar da jami’an tsaro da wasu jami’an gwamnati.

Shugaban hukumar Barrister Muhyi Magaji Rimingado, ne ya sanar da hakan, yayin wani taron tuntuba da hukumar ta gudanar a ranar Talata. 

Rimingado, ya ce an samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bisa aikin hadin gwiwa tsakanin hukumar da jami’an tsaro da ma’aikatar kasa da jami’an ma’aikatar sharia da na kotu, inda ya bayyana kokarin da hukumar ke yi wajen ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu a irin wannan badakala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara