DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kirsimeti: Kungiyar kiristocin Nijeriya ta bukaci Tinubu ya rage farashin kayan abinci

-

Kungiyar kiristocin Nijeriya ta bukaci Tinubu ya rage farashin kayan abinci

Kungiyar kiristocin Nijeriya CAN ta bukaci gwamnatin tarayya da ta karfafa bangaren aikin gona da kuma rage farashin kayan abinci tare kuma da samar da daidaito a tsakanin yan kasa.

Shugaba Kungiyar Archbishop Daniel Okoh, ne ya mika wannan bukata a sakonsa na Kirsimeti ga mabiya addinin kirista, inda ya bukaci kiristoci da su rubanya riko da koyarwar Yesu domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma musamman a irin wannan lokaci na tsanani.

Ya kuma nuna alhininsa game da yadda bikin na bana ya zo da wani irin yanayi na tausayi, musamman ganin yadda mutane suka rasa rayukansu a turmutsitsin karbar sadaka da ya gudana a Abuja da Ibadan da kuma Anambra.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Farashin buhun shinkafar waje mai nauyin 50KG ya koma N58,000 a wasu sassan Nijeriya in ji wani rahoton da majiyar DCL Hausa ta Punch ta wallafa.

Rahoton da kamfanin S&P Global ya fitar ya bayyana cewa farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka zuwa N58,000 a wasu yankunan Najeriya,...

‘Yan siyasar da ke neman mukamai ba don talakawa suke yi ba – Zargin Bafarawa ga ‘yan siyasar Nijeriya

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi zargin cewa an yi wa siyasar adawa kamshin mutuwa a Najeriya. Bafarawa, wanda ya kasance jigo...

Mafi Shahara