Sojoji sun hallaka dan ta’adda Alhaji Ma’oli, dake kakabawa al’ummar Zamfara haraji

-

Runduna ta 1 ta dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, ta hallaka ‘yan bindiga da dama a jihar Zamfara, ciki har da wani kasurgumin dan bindiga Alhaji Ma’oli.
A yayin wani farmaki da ta kai ne a kauyen Mai Sheka kusa ga kauyen Kunchin Kalgo, rundunar ta gama da ɗan ta’adda Ma’oli, wanda ya yi suna wajen kakabawa al’ummomi haraji da suka hada da Unguwan Rogo, Mai Sheka, Magazawa, da yankunan Bilbis cikin karamar hukumar Tsafe.
Wani bayani da Kodinetan yada labarai na 
Rundunar Operation Fansan Yamma, Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce an kai harin ne bayan samun bayanan da suka nuna cewa an ga ‘yan bindigar saman babura a yankin karamar hukumar Tsafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara