Gwamnatin Nijeriya za ta yi wa yara sama da miliyan 10 rejistar haihuwa cikin watanni 3

-

Hukumar kidayar jama’a ta Nijeriya ta ce za a yi wa yara sama da miliyan 10 rejistar haihuwa a cikin watanni uku.
Shugaban hukumar Alhaji Nasir Isa Kwara, ne ya bayyana hakan jim kaÉ—an bayan da uwar gidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta gabatar da takardar haihuwa ga jariri na farko da aka haifa a sabuwar shekarar 2025.
Alhaji Nasir wanda ya samu wakilcin Kwamishinan hukumar a jihar Katsina, Bala Banya, ya ce hukumar kidaya ta dukufa don tabbatar da cewa kowane yaro an yi masa rejista a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara